Amma shugaban majami'a ya ji haushi, don Yesu ya warkar ran Asabar. Sai ya ce wa jama'a, “Akwai ranaku har shida da ya kamata a yi aiki. Ku zo mana a ranakun nan a warkar da ku, ba ran Asabar ba.”
“Cikin kwana shida za ku yi aikinku, amma a kan rana ta bakwai sai ku huta, don shanunku da jakunanku su kuma su huta, don bayinku da baƙinku su wartsake.
Cikin kwanaki shida za a yi aiki, amma a rana ta bakwai za a huta ɗungum, gama ranar Asabar ce, tsattsarka. Ko kaɗan ba za a yi aiki a ranar ba a duk inda suke, amma ku yi taruwa ta sujada gama ranar Asabar ta Ubangiji ce.
Cikin kwana shida za a yi aiki, amma rana ta bakwai Asabar ce tsattsarka ta Ubangiji ta hutawa sosai. Duk wanda ya yi kowane irin aiki a cikinta, sai a kashe shi.
A kwana shida za a yi aiki, amma rana ta bakwai ranar hutawa ce tsattsarka ta saduda ga Ubangiji, don haka duk wanda ya yi kowane irin aiki a cikinta za a kashe shi.
“Ni Ubangiji Allah na ce za a rufe ƙofar fili ta can ciki wadda take fuskantar gabas dukan ranaku shida na aiki, amma za a buɗe ta a ranar Asabar da a amaryar wata.