Na yi ta aiko muku da bayina annabawa, ina cewa, kowa ya bar muguwar hanyarsa, ya gyara ayyukansa, kada ya bauta wa gumaka. Ta haka za ku zauna a ƙasa wadda na ba ku, ku da kakanninku, amma ba ku kasa kunne, ku ji ni ba.
duk da haka dai, a gare mu kam, Allah ɗaya ne, wato Uba, wanda dukkan abubuwa suke daga gare shi, wanda mu kuma zamansa muke yi, Ubangiji kuma ɗaya ta gare shi muka kasance.
Sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada, amma, sai ya ce mini, “Ko kusa kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da 'yan'uwanka, waɗanda suke shaidar Yesu. Allah za ka yi wa sujada.” Domin gaskiyar da Yesu ya bayyana ita ce ta ba da ikon yin annabci.
Kada ku yarda kowane mutum ya ɓata ku, da cewa shi wani abu ne saboda, ya ga wahayi, ya kuma lazamta da yin tawali'un ƙarya, in ji shi kuma yana yi wa mala'iku sujada. Irin wannan mutum kumbura kansa yake yi ba dalili, sai ta son zuciya irin na halin mutuntaka,
Kun dai tabbata, ba wani fasiki, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayi (wanda shi da mai bautar gumaka duk ɗaya ne), da yake da gādo a mulkin Almasihu da na Allah.
Ya jama'ata, kada ku ji tsoro! Kun sani tun daga zamanin dā can, har zuwa yanzu, Na faɗa tun da wuri abin da zai faru. Ku ne kuwa shaiduna! Ko akwai wani Allah? Ko akwai wani Allah mai iko da ban taɓa jin labarinsa ba?”
“Ya jama'ar Isra'ila, ku ne shaiduna, Na zaɓe ku al'umma, baiwata, Domin ku san ni, ku gaskata ni, Ku kuma fahimta, ni kaɗai ne Allah. In banda ni ba wani Allah, Ba a taɓa yin wani ba, Ba kuwa za a yi ba.
Amma, sai ya ce mini, “Ko kusa kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da 'yan'uwanka annabawa, da kuma waɗanda suke kiyaye maganar littafin nan. Allah za ka yi wa sujada.”
Sun yi saurin kaucewa daga hanyar da na umarce su. Sun yi wa kansu ɗan maraƙi na zubi, sun yi masa sujada, sun miƙa masa hadaya, sun kuma ce, ‘Ya Isra'ila, wannan shi ne allahn da ya fisshe ka daga ƙasar Masar’ ”
sa'ad da Sulemanu ya tsufa sai suka janye zuciyarsa zuwa bin waɗansu gumaka, bai bi Ubangiji Allahnsa da zuciya ɗaya kamar yadda tsohonsa, Dawuda, ya yi ba.