Ya ku 'yan'uwana, kada ku kushe wa juna. Kowa ya kushe wa ɗan'uwansa, ko ya ɗora masa laifi, ya kushe wa shari'a ke nan, ya kuma ɗora mata laifi. In kuwa ka ɗora wa shari'a laifi, kai ba mai binta ba ne, mai ɗora mata laifi ne.
Kada ku yi ta yaɗa ƙarya game da wani. Sa'ad da wani yake cikin shari'ar kuɓutar da ransa, ku yi magana muddin dai shaidarku za ta taimake shi. Ni ne Ubangiji.