Umarnan nan cewa, “kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka yi ƙyashi,” da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma cewa, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”
Domin shi wannan da ya ce, “Kada ka yi zina,” shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisankai.” To, in ba ka yi zina ba amma ka yi kisankai, ai, ka zama mai keta Shari'a ke nan.
yana kuma tunawa, cewa ita Shari'a ba a kafa ta domin masu adalci ba, sai dai kangararru, da marasa biyayya, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa tsarkaka, da masu saɓon Allah, da masu kashe iyaye maza da mata, da masu kisankai,
Ubangiji yana zuwa ya hukunta jama'arsa a duniya saboda zunubansu. Kashe-kashen da aka yi a duniya a ɓoye, za a bayyana su, ƙasa ba za ta ƙara ɓoye waɗanda aka kashe ba.
da hassada, da buguwa, da shashanci, da kuma sauran irinsu. Ina faɗakar da ku kamar yadda na faɗakar da ku a dā, cewa masu yin irin waɗannan abubuwa, ba za su sami gādo a Mulkin Allah ba.
Da mutanen garin suka ga mugun ƙwaron nan a makale a hannun Bulus, suka ce wa juna, “Lalle mutumin nan mai kisankai ne, kun ga ko da yake ya tsira daga bahar, duk da haka alhaki yana binsa sai ya mutu.”
Ku tabbata dai, idan kuka kashe ni, za ku jawo hakkin jinin marar laifi a kanku da a kan wannan birni da mazauna a cikinsa, gama a gaskiya Ubangiji ne ya aiko ni wurinku domin in faɗa muku dukan maganan nan a kunnuwanku.”
Sarki Yowash bai tuna da irin alherin da Yehoyada mahaifin Zakariya ya yi masa ba, amma ya kashe ɗansa. Sa'ad da Zakariya yake bakin mutuwa, sai ya ce, “Bari Ubangiji ya gani ya kuma sāka.”
Banda wannan kuma Manassa ya kashe adalai har ya cika Urushalima daga wannan gefe zuwa wancan da jininsu, banda zunubin da ya sa mutanen Yahuza su yi, har suka aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji.
Amma idan san ya saba fafarar mutane, aka kuma yi wa mai shi kashedi, amma bai kula ba, har san ya kashe ko mace ko namiji, sai a jajjefi san duk da mai shi.
Ka dai san umarnan nan, ‘Kada ka yi kisankai. Kada ka yi zina. Kada ka yi sata. Kada ka yi shaidar zur. Kada ka yi zamba. Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”