“Ubangiji ya faɗa wa taron jama'arku waɗannan dokoki da murya mai ƙarfi ta tsakiyar wuta, da girgije, da duhu baƙi ƙirin. Ya rubuta su a bisa alluna biyu na dutse, ya ba ni, ba abin da ya ƙara.”
Shi ne kuma wanda yake a cikin Ikkilisiyar nan a jeji tare da mala'ikan da ya yi masa magana a Dutsen Sinai, tare da kakanninmu kuma. Shi ne kuma ya karɓo rayayyiyar magana domin ya kawo mana.
Ubangiji kuwa ya sāke rubuta dokoki goma a allunan kamar na farko, wato dokoki goma ɗin nan da Ubangiji ya faɗa muku a dutse ta tsakiyar wuta a ranar taron. Sai Ubangiji ya ba ni su.