Fitowa 2:3 - Littafi Mai Tsarki3 Da ta ga ba za ta iya ƙara ɓoye shi ba, sai ta saƙa kwando da iwa, ta yaɓe shi da katsi, ta sa jaririn a ciki, ta ajiye shi cikin kyauro a bakin Kogin Nilu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 Amma da ba tă iya ɓoye shi kuma ba, sai ta yi kwandon kyauro ta shafa masa kwalta. Bayan haka sai ta sa jaririn a cikin kwandon, ta je ta ajiye kwandon tare da jaririn a cikin kyauro, a bakin kogin. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Daga waccan ƙasar wakilai sukan gangaro daga Kogin Nilu a cikin jiragen ruwa da aka yi da iwa. Ku koma gida, ku manzanni masu gaggawa! Ku kai saƙo ƙasarku, can a mafarin Kogin Nilu, zuwa ga al'ummarku mai ƙarfi mai iko, zuwa ga dogayen mutanenku masu sulɓin jiki, waɗanda ake jin tsoronsu ko'ina a duniya.