Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Fitowa 19:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Isra'ilawa sun kai jejin Sina'i a farkon watan uku bayan fitowarsu daga ƙasar Masar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 A rana ta farko a cikin watan uku bayan da Isra’ilawa suka bar Masar, a wannan rana, suka iso Hamadar Sinai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Fitowa 19:1
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Taron jama'ar Isra'ila suka tashi daga Elim suka shiga jejin Sin wanda yake tsakanin Elim da Sina'i, a rana ta goma sha biyar ga watan biyu bayan fitowarsu daga ƙasar Masar.


Za ku turke dabbar har rana ta goma sha huɗu ga wata, wato sa'ad da dukan taron jama'ar Isra'ila za su yanka ragunansu da maraice.


Suka tashi daga Refidim suka sauka a jejin Sinai.


wannan wata zai zama wata na farko a shekara a gare su.


Sai Allah ya ce, “Zan kasance tare da kai, wannan kuwa zai zama alama a gare ka, cewa ni ne na aike ka. Sa'ad da ka fito da jama'ar daga Masar, za ku bauta wa Allah a bisa dutsen nan.”


A wannan rana ce Ubangiji ya fitar da Isra'ilawa runduna runduna daga ƙasar Masar.


“A kan rana ta fari ga wata na fari za ka kafa alfarwa ta sujada.


Ubangiji ya yi magana da Musa a jejin Sinai, ya ce masa


“Ubangiji Allahnmu ya faɗa mana a Horeb, ya ce, ‘Daɗewarku a wannan dutse ta isa.


da yadda kuma a waccan rana kuka tsaya a gaban Ubangiji Allahnku a Horeb, sa'ad da Ubangiji ya ce mini, ‘Ka tattara mini jama'a domin su ji maganata, su koyi tsorona dukan kwanakinsu a duniya, su kuma koya wa 'ya'yansu.’


“Domin haka, sai ku kula da kanku sosai, gama ba ku ga siffar kome ba sa'ad da Ubangiji Allahnku ya yi magana da ku a Horeb ta tsakiyar wuta.


Ubangiji Allahnmu ya yi alkawari da mu a Horeb.


“Sai na fisshe su daga ƙasar Masar, na kawo su cikin jeji.


A rana ta fari ga wata na biyu a shekara ta biyu bayan da Isra'ilawa suka bar Masar, Ubangiji ya yi magana da Musa a cikin alfarwa ta sujada a jejin Sinai. Ya ce,


Isra'ilawa kuwa suka tashi daki-daki daga jejin Sinai. Girgijen kuma ya tsaya a jejin Faran.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ