Fitowa 18:8 - Littafi Mai Tsarki8 Sai Musa ya faɗa wa surukinsa dukan abin da Ubangiji ya yi da Fir'auna da Masarawa saboda Isra'ilawa, ya kuma faɗa masa dukan wahalar da suka sha a kan hanya, da yadda Ubangiji ya cece su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20208 Musa kuwa ya faɗa wa surukinsa duk abubuwan da Ubangiji ya yi wa Fir’auna da Masarawa domin Isra’ila, da batun wahalolin da suka sha a hanya, da yadda Ubangiji ya cece su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Ya Allah, Allahnmu, da girma kake! Kai mai banrazana ne, cike da iko! Da aminci ka cika alkawaranka da ka alkawarta. Daga lokacin da Sarkin Assuriya ya danne mu, Har yanzu ma, wace wahala ce ba mu sha ba! Sarakunanmu, da shugabanninmu, da firistocinmu, Da annabawanmu, da kakanninmu, Da dukan sauran jama'arka sun sha wahala. Ka san irin wahalar da muka sha.