Sa'ad da Dawuda da mutanensa suka koma Ziklag a rana ta uku, sai suka tarar Amalekawa sun riga sun kawo wa Negeb da Ziklag hari. Suka cinye Ziklag, suka ƙone ta.
Dukan taron jama'ar Isra'ila suka tashi daga jejin Sin, suna tafiya daga zango zuwa zango bisa ga umarnin Ubangiji. Suka yi zango a Refidim, amma ba ruwan da jama'a za su sha.
Dawuda yakan fita da mutanensa su kai wa Geshurawa, da Girziyawa, da Amalekawa hari. Waɗannan su ne mazaunan ƙasar a dā, tun daga Shur har zuwa ƙasar Masar.
Amalekawa suna zaune a Negeb, Hittiyawa kuwa, da Yebusiyawa, da Amoriyawa suna zaune a ƙasar tuddai, Kan'aniyawa suna zaune kusa da teku, da kuma kusa da Kogin Urdun.”