Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Fitowa 17:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Zan tsaya a dutsen Horeb can a gabanka. Za ka bugi dutsen, ruwa kuwa zai fito domin jama'a su sha.” Musa kuma ya yi haka nan a gaban dattawan Isra'ila.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Zan tsaya a can a gabanka, kusa da dutsen Horeb. Ka bugi dutsen, ruwa kuwa zai fito daga gare shi domin mutane su sha.” Sai Musa ya yi haka a idon dattawan Isra’ila.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Fitowa 17:6
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

duk kuma sun sha ruwan nan na ruhu. Domin sun sha ruwa daga Dutsen nan na ruhu, wanda ya yi tafiya tare da su. Dutsen nan kuwa Almasihu ne.


Ka ba su abinci daga sama sa'ad da suka ji yunwa, Ruwa kuma daga dutse sa'ad da suka ji ƙishi, Ka faɗa musu su shiga su mallaki ƙasar da ka yi alkawari za ka ba su.


Ubangiji ya bishe ku cikin babban jejin nan mai bantsoro, ƙasa mai macizai masu zafin dafi, da kunamai, da busasshiyar ƙasa wadda ba ta da ruwa. Ubangiji kuwa ya ba ku ruwa daga dutsen ƙanƙara.


Ya buɗe dutse, sai ruwa ya bulbulo, Yana gudu cikin hamada kamar kogi.


Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda ya ce miki, ‘Sa mini ruwa in sha,’ ai, da kin roƙe shi, shi kuwa zai ba ki ruwan rai.”


Wanda ya sa duwatsu su zama tafkunan ruwa, Ya kuma sa kogwannin duwatsu su zama maɓuɓɓugai, Masu bulbulo da ruwa.


Akwai kogin da yake kawo farin ciki a birnin Allah, Da cikin tsattsarkan Haikali na Maɗaukaki.


Gaskiya ce, ya bugi dutse, Ruwa kuwa ya fito a yalwace, Amma ko yana da iko ya ba da abinci da nama ga jama'arsa?”


Ruhu da amarya suna cewa, “Zo.” Duk wanda ya ji kuwa, yă ce, “Zo.” Duk mai jin ƙishirwa ya zo, duk mai bukata, yă ɗibi ruwan rai kyauta.


Amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada. Ruwan da zan ba shi kuwa zai zama maɓuɓɓuga a gare shi, yana ɓuɓɓugowa har ya zuwa rai madawwami.”


Lokacin da Ubangiji ya bi da mutanensa ta cikin busasshiyar hamada, mai zafi, Ba su sha wahalar ƙishi ba. Ya sa ruwa ya gudano daga cikin dutse dominsu, Ya tsage dutse, ruwa ya kwararo.


Sa'ad da Haruna yake magana da taron jama'ar, suka duba wajen jeji, sai ga ɗaukakar Ubangiji ta bayyana a cikin girgije.


Ɗaga sandanka, ka miƙa hannunka a bisa bahar, ka raba shi, domin Isra'ilawa su taka busasshiyar ƙasa cikin bahar, su haye.


“Ka ɗauki sandanka, kai da Haruna, ɗan'uwanka, ku tara jama'a, ku yi magana da dutsen a gabansu ya ba da ruwan da yake cikinsa. Za ka sa ruwa ya ɓuɓɓugo musu daga dutsen. Ta haka za ka ba taron jama'a da garkunansu ruwan sha.”


Tafiyar kwana goma sha ɗaya ne daga Horeb zuwa Kadesh-barneya, ta hanyar Dutsen Seyir.


Ka sa ruwan maɓuɓɓugai ya yi gudu, Ka sa manyan koguna su ƙafe.


Da gangan suka jarraba Allah, Da suka ce ya ba su irin abincin da suke so.


Sa'ad da kuke shan wahala Kuka yi kira a gare ni, na kuwa cece ku. Daga maɓuyata cikin hadiri, na amsa muku, Na jarraba ku a maɓuɓɓugan Meriba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ