Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Fitowa 17:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Domin haka jama'a suka zargi Musa suka ce, “Ba mu ruwa, mu sha.” Musa ya amsa musu ya ce, “Don me kuke zargina? Don me kuke gwada Ubangiji?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Saboda haka suka yi wa Musa maganganun banza suka ce, “Ba mu ruwa mu sha.” Musa ya amsa ya ce, “Don me kuke mini maganganun banza? Don me kuke gwada Ubangiji?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Fitowa 17:2
32 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kada kuma mu gwada Ubangiji yadda waɗansu suka yi, har macizai suka hallaka su.


Suka yi ta jarraba Allah a kai a kai, Suka kuwa sa Mai Tsarki na Isra'ila yin fushi.


Da gangan suka jarraba Allah, Da suka ce ya ba su irin abincin da suke so.


“Kada ku gwada Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka yi a Masaha.


A inda kakanninku suka gwada ni, suka jarraba ni, Suna ganin ayyukana har shekara arba'in.


Ahaz ya amsa, ya ce, “Ba zan nemi wata alama ba. Ba zan jarraba Ubangiji ba.”


Sai Yesu ya ce masa, “A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”


A can suka gwada ni suka jarraba ni, Ko da yake da idanunsu suka ga abin da na yi dominsu.


Suka yi wa Allah gunaguni, da Musa kuma, suka ce, “Me ya sa kuka fitar da mu daga Masar, kuka kawo mu cikin jeji mu mutu? Gama ba abinci, ba ruwa, mu kuwa mun gundura da wannan abinci marar amfani.”


Saboda haka, don me kuke gwada Allah, ta ɗora wa almajiran nan kayan da mu, duk da kakanninmu, muka kasa ɗauka?


Amma Bitrus ya ce mata, “Ƙaƙa kuka gama baki ku gwada Ruhun Ubangiji? Kin ji tafiyar waɗanda suka binne mijinki, har sun iso bakin ƙofa ma, za su kuwa ɗauke ki, su fitar da ke.”


Sai Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai kuwa an ce, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”


A ganinmu masu girmankai suna jin daɗi. Masu aikata mugunta kuwa ba arziki kaɗai suke yi ba, amma sukan jarraba Allah da mugayen ayyukansu su kuwa zauna lafiya.’ ”


Suka cika da sha'awa cikin hamada, Suka jarraba Allah,


Amma sai suka yi wa Allah Mai Iko Dukka tawaye, Suka jarraba shi. Ba su kiyaye dokokinsa ba,


dukan mutanen da suka ga ɗaukakata da alamuna waɗanda na aikata a Masar, da kuma a jejin, suka kuwa jarraba ni har sau goma, ba su kuma yi biyayya da maganata ba,


Sai aka sa wa wurin suna, “Masaha” da “Meriba”, saboda Isra'ilawa suka yi husuma, suka kuma jarraba Ubangiji suna cewa, “Ubangiji yana tare da mu, ko babu?”


Sai ƙaramin ya ce wa ubansa, ‘Baba, ba ni rabona na gādo.’ Sai uban ya raba musu dukiyarsa.


Sai mutanen suka yi wa Musa gunaguni suna cewa, “Me za mu sha?”


Amma Sama'ila bai ji daɗin roƙonsu ba, na a naɗa musu sarki, saboda haka ya yi addu'a ga Ubangiji.


Dukan Isra'ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna, suke ce, “Da ma mun mutu a ƙasar Masar, ko kuwa a wannan jeji.


Suka ce wa Musa da Haruna, “Allah ya duba, ya hukunta ku, gama kun sa mun yi baƙin jini a wurin Fir'auna da barorinsa, har suka ɗauki takobi don su kashe mu.”


Musa ya kuma ce, “Da yamma Ubangiji zai ba ku nama ku ci, da safe kuwa zai ƙosar da ku da abinci, gama Ubangiji ya riga ya ji irin gunagunin da kuka yi a kansa. Ai, gunagunin ba a kanmu yake ba, wane mu? A kan Ubangiji ne kuka yi.”


“Kada ku taurare zuciyarku yadda kakanninku suka yi a Meriba, Kamar yadda suka yi a jeji a Masaha, a wancan rana.


Amma nan da nan, suka manta da abin da ya yi, Suka aikata, ba su jira shawararsa ba.


“Kun kuma tsokano Ubangiji ya husata a Tabera, da a Masaha, da a Kibrot-hata'awa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ