Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Fitowa 17:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Joshuwa kuwa ya yi yadda Musa ya faɗa masa, ya fita ya yi yaƙi da Amalekawa. Musa, da Haruna, da Hur kuma suka hau kan dutsen.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Sai Yoshuwa ya yaƙi Amalekawa kamar yadda Musa ya umarta, Musa, Haruna da Hur kuwa suka tafi bisa tudu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Fitowa 17:10
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya ce wa dattawan, “Ku dakata a nan har mu komo wurinku. Haruna da Hur suna tare da ku, in wani yana da wata damuwa, sai ya je wurinsu.” Sa'an nan Musa ya hau bisa dutsen.


Sun yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa bawansa, haka kuma Musa ya umarci Joshuwa, haka kuwa Joshuwa ya yi. Ba abin da bai aikata ba cikin dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa.


“Ga shi, na zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuza.


Sa'ad da hannuwan Musa suka gaji, Haruna da Hur suka ɗauki dutse suka ajiye wa Musa, ya zauna a kai, su kuwa suka tsaya a gefen damansa da hagunsa suna tallabe da hannunsa sama, suka tallabe su har faɗuwar rana.


Ku aminaina ne in kuna yin abin da na umarce ku.


Sai uwa tasa ta ce wa barorin, “Duk abin da ya ce ku yi, sai ku yi.”


kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku. Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har zuwa matuƙar zamani.”


Muddin hannun Musa na miƙe, sai Isra'ilawa su yi ta cin nasara, amma da zarar hannunsa ya sauka, sai Amalekawa su yi ta cin nasara.


Sa'ad da Azuba ta rasu sai Kalibu ya auri Efrata wadda ta haifa masa Hur.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ