Ka yi hanya ta cikin teku domin jama'arka, Ka sa su bi ta ciki a kan sandararriyar ƙasa. Ka sa waɗanda suke fafararsu suka hallaka cikin zurfin teku, Suka nutse kamar dutse.
Sai wani ƙaƙƙarfan mala'ika ya ɗauki wani dutse kamar babban dutsen niƙa, ya jefa a teku, ya ce, “Haka za a fyaɗa Babila babban birni, da ƙarfi, ba kuwa za a ƙara ganinta ba.
Amma fa duk wanda ya sa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara masu gaskatawa da ni ya yi laifi, zai fiye masa a rataya babban dutsen niƙa a wuyarsa, a kuma nutsar da shi a zurfin teku.”
Tsoro da razana sun aukar musu, Ta wurin ikonka suka tsaya cik kamar dutse, Har jama'arka, ya Ubangiji, suka haye, I, jama'arka, ya Ubangiji, suka haye,