Ku yi kururuwa, ku yi kuka na neman taimako, dukanku biranen Filistiya! Ku razana dukanku! Ƙurar da ta murtuke tana zuwa daga arewa, mayaƙa ne, ba kuwa matsorata a cikinsu.
Sai suka amsa wa Joshuwa, suka ce, “Domin bayinka sun ji labari Ubangiji Allahnka ya umarci bawansa Musa ya ba ku ƙasar duka, ku hallaka dukan mazaunan ƙasar a gabanku, don haka muka ji tsoronku ƙwarai saboda rayukanmu, shi ya sa muka yi haka.
Za su kuwa faɗa wa mutanen wannan ƙasa, gama sun riga sun ji, kai, ya Ubangiji, kana cikin tsakiyar jama'ar nan wadda kake bayyana kanka gare ta fuska da fuska. Girgijenka kuma yana tsaye a kansu, kakan kuma yi musu jagora da al'amudin wuta.
Ku mutanen Filistiya, sandan da ake dūkanku da shi ya karye, amma kada wannan ya zamar muku dalilin murna. Gama idan wani maciji ya mutu, wani mafi mugunta zai maye gurbinsa. Ƙwan maciji yake ƙyanƙyashe maciji mai tashi sama!
ya aiki manzanni zuwa wurin Bal'amu ɗan Beyor a Fetor, a ƙasar danginsa, wadda take kusa da kogin, su kirawo shi, su ce, “Ga mutane sun fito daga ƙasar Masar, sun mamaye ƙasar, ga shi, suna zaune daura da ni.
Da muka ji, sai zukatanmu suka narke, har ba sauran ƙarfin hali da ya ragu a kowane mutum saboda ku. Gama Ubangiji Allahnku shi ne Allahn da yake a Sama daga bisa, da duniya a ƙasa.
Suka amsa masa suka ce, “Daga ƙasa mai nisa ƙwarai, bayinka suka zo saboda sunan Ubangiji Allahnka, gama mun ji labarinsa da dukan abin da ya yi a Masar,
Ya tsaya, ya auna duniya, Ya duba, sai ya girgiza al'umman duniya. Sa'an nan madawwaman duwatsu suka farfashe, Madawwaman tuddai kuma suka zama bai ɗaya. Haka hanyoyinsa suke tun adun adun.