6 Ya kuwa shirya karusarsa, ya ɗauki rundunarsa tare da shi.
6 Sai shi da keken yaƙinsa suka shirya, ya kuma ɗauki sojojinsa tare da shi.
Da aka faɗa wa Sarkin Masar jama'a sun gudu, sai shi da fādawansa suka sāke tunaninsu game da jama'ar, suka ce, “Me muka yi ke nan, da muka bar Isra'ilawa su fita daga cikin bautarmu?”
Ya kuma ɗauki zaɓaɓɓun karusai ɗari shida da sauran karusan Masar duka waɗanda shugabanni suke bi da su.
“Karusan Fir'auna da rundunarsa, ya jefar cikin bahar, Zaɓaɓɓun jarumawansa ya nutsar da su cikin Bahar Maliya.