Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Fitowa 13:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Sai ku kiyaye wannan farilla a wannan wata sa'ad da Ubangiji ya kai ku ƙasar Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, wadda ya rantse wa kakanninku zai ba ku, wato ƙasar da take ba da yalwar abinci.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Sa’ad da Ubangiji ya kawo ku cikin ƙasar Kan’aniyawa, Hittiyawa, Amoriyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa, ƙasar da ya rantse wa kakanninku cewa zai ba ku, ƙasar da take zub da madara da zuma, za ku kiyaye wannan biki a wannan wata.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Fitowa 13:5
31 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

don haka na sauko in cece su daga hannun Masarawa, in fito da su daga cikin wannan ƙasa zuwa kyakkyawar ƙasa mai ba da yalwar abinci, wato ƙasar Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.


Da kuka haye Urdun, kuka zo Yariko, mutanen Yariko kuwa suka yi yaƙi da ku, haka kuma Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Kan'aniyawa da Hittiyawa, da Girgashiyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, amma na ba da su a gare ku.


Sa'an nan zan kawo ku cikin ƙasar da na rantse zan bai wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. Zan ba ku ita ta zama mallakarku. Ni ne Ubangiji.’ ”


Ku kiyaye abin da na umarce ku a wannan rana. Ga shi, zan kora muku Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.


Ya yi alkawari cewa zai fisshe ku daga wahalar Masar zuwa ƙasar Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa. Ƙasa wadda take mai ba da yalwar abinci.’


“Sa'ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku gāda, kuka mallake ta, kuka zauna cikinta,


“Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya hallaka al'ummai waɗanda zai ba ku ƙasarsu, sa'ad da kuka kore su, kuka zauna cikin garuruwansu da gidajensu,


“Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kawar muku da al'umman nan waɗanda za ku shiga ƙasarsu don ku kore su, sa'ad da kuka kore su, kun zauna a ƙasarsu,


“Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku ƙasar da kuke shiga ku mallake ta, zai korar muku da al'ummai da yawa, su Hittiyawa, da Girgashiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, al'umma bakwai ke nan, waɗanda suka fi ku yawa, da kuma ƙarfi.


‘Hakika ba wani daga cikin mutanen da suka fito daga Masar, tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba da zai ga ƙasar da na rantse zan ba Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, domin ba su bi ni sosai ba.


ba wanda zai shiga ƙasar da na rantse ta zama wurin zamanku, sai Kalibu, ɗan Yefunne, da Joshuwa ɗan Nun.


‘Domin Ubangiji ya kāsa kai jama'ar nan zuwa cikin ƙasar da ya rantse zai ba su, don haka ya kashe su a cikin jeji.’


Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi, ka kama hanya, kai da jama'ar da ka fisshe su daga ƙasar Masar, zuwa ƙasar da na rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, na ce, ‘Ga zuriyarka zan ba da ita.’


Yusufu kuwa ya ce wa 'yan'uwansa, “Ina gab da mutuwa, amma lalle Allah zai ziyarce ku, zai kuwa haurar da ku daga wannan ƙasa zuwa ƙasar da ya rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.”


Ka yi baƙunci cikin wannan ƙasa, ni kuwa zan kasance tare da kai, zan sa maka albarka, gama a gare ka da zuriyarka ne na ba da waɗannan ƙasashe, zan kuwa cika rantsuwar da na yi wa Ibrahim mahaifinka.


Za ku kiyaye waɗannan ƙa'idodi, ku riƙe su farilla, ku da 'ya'yanku har abada.


Sai ku kiyaye farillan nan kowace shekara a lokacinta.”


“Sa'ad da Ubangiji ya kai ku ƙasar Kan'aniyawa wadda zai ba ku kamar yadda ya rantse muku, ku da kakanninku,


Ka tuna da bayinka Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, waɗanda kai da kanka ka rantse musu, ka ce, ‘Zan riɓaɓɓanya zuriyarku kamar taurarin sama, in kuma ba ku wannan ƙasa duka da na alkawarta zan bayar ga zuriyarku. Za su kuwa gāje ta har abada’ ”


Amma ni na faɗa muku, za ku gāji ƙasarsu, zan kuwa ba ku ita, ku mallake ta, ƙasar da take da yalwar abinci. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya keɓe ku daga sauran al'ummai.


Ni na ɗauki cikinsu? Ko kuwa ni ne na haife su, har da za ka ce mini, ‘Ka ɗauke su a ƙirjinka, kamar yadda mai reno yake rungume jariri, zuwa ƙasa wadda ka rantse za ka bai wa kakanninsu?’


Suka ce wa Musa, “Mun tafi ƙasar da ka aike mu, ƙasar tana da yalwar abinci, ga kuma amfanin ƙasar.


Sa'an nan zan cika maganar rantsuwa da na rantse wa kakanninku, da na ce zan ba su ƙasa wadda take cike da albarka kamar yadda yake a yau.’ ” Irmiya ya ce, “Amin, amin, ya Ubangiji.”


Ka kuwa ba su wannan ƙasa wadda ka rantse za ka ba kakanninsu. Ƙasar da take cike da yalwar albarka.


a ran nan na rantse musu, cewa zan fito da su daga ƙasar Masar, zuwa wata ƙasa wadda na samo musu, ƙasar da take da yalwar albarka, wato ƙasa mai albarka duka.


Na kuma yi musu alkawari zan ba su ƙasar Kan'ana, inda suka yi zaman baƙunci.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ