Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Fitowa 12:51 - Littafi Mai Tsarki

51 A wannan rana ce Ubangiji ya fitar da Isra'ilawa runduna runduna daga ƙasar Masar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

51 A wannan rana, Ubangiji ya fito da Isra’ilawa ɓangare-ɓangare daga Masar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Fitowa 12:51
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A ranar da shekara arbaminya da talatin ɗin nan suka cika, a ran nan ne dukan rundunar Ubangiji suka fita daga ƙasar Masar.


Wannan Haruna ne da Musa, waɗanda Ubangiji ya yi musu magana su fito da Isra'ilawa daga cikin ƙasar Masar, ƙungiya ƙungiya.


Allahn jama'ar nan Isra'ila ya zaɓi kakanninmu, ya ɗaukaka jama'ar sa'ad da suke baƙunci a ƙasar Masar, da maɗaukakin iko kuma ya fito da su daga cikinta.


Sai dai ina so in tuna muku, ko da yake kun riga kun san kome sosai, cewa Ubangiji ya ceci jama'a daga ƙasar Masar, duk da haka daga baya ya hallaka waɗanda ba su ba da gaskiya ba.


don haka na sauko in cece su daga hannun Masarawa, in fito da su daga cikin wannan ƙasa zuwa kyakkyawar ƙasa mai ba da yalwar abinci, wato ƙasar Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.


Sai ka faɗa wa Isra'ilawa cewa, ‘Ni Ubangiji zan 'yantar da ku daga wulakancin nan da Masarawa suke yi muku. Zan kuɓutar da ku daga bautar Masarawa. Da ƙarfi zan aikata hukuntaina masu iko don in cece ku.


Amma Fir'auna ba zai kasa kunne gare ku ba, don haka zan miƙa hannuna a bisa Masar, zan fitar da rundunar jama'ata, wato Isra'ilawa, daga ƙasar Masar ta wurin hukuntaina masu iko.


Isra'ilawa suka yi na'am da shi, suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa da Haruna.


Taron jama'ar Isra'ila suka tashi daga Elim suka shiga jejin Sin wanda yake tsakanin Elim da Sina'i, a rana ta goma sha biyar ga watan biyu bayan fitowarsu daga ƙasar Masar.


Isra'ilawa sun kai jejin Sina'i a farkon watan uku bayan fitowarsu daga ƙasar Masar.


Sa'ad da jama'ar Isra'ila suka bar Masar, Sa'ad da zuriyar Yakubu suka bar baƙuwar ƙasar nan,


Shi ya fito da jama'ar Isra'ila daga cikin Masar, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.


Na fito da ku, wato jama'ata daga Masar. Na bi da ku cikin jeji shekara arba'in, Na kuwa ba ku ƙasar Amoriyawa ta zama taku.


Gama na fito da ku daga ƙasar Masar, Na fanshe ku daga gidan bauta. Na aika muku da Musa, da Haruna, da Maryamu.


Yusufu kuwa ya ce wa 'yan'uwansa, “Ina gab da mutuwa, amma lalle Allah zai ziyarce ku, zai kuwa haurar da ku daga wannan ƙasa zuwa ƙasar da ya rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.”


Don zuriyarsu ta sani Ubangiji ya sa Isra'ilawa su zauna cikin bukkoki, sa'ad da ya fito da su daga ƙasar Masar. Shi ne Ubangiji Allahnsu.


Allah ne ya fisshe shi daga Masar, Ya yi yaƙi dominsu kamar kutunkun ɓauna.


“A ƙidaya mutane tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba kamar yadda Ubangiji ya umarta.” Isra'ilawa waɗanda suka fita daga ƙasar Masar ke nan.


Waɗannan su ne wuraren da Isra'ilawa suka yi zango sa'ad da suka fita runduna runduna daga ƙasar Masar ta hannun Musa da Haruna.


Saboda ya ƙaunaci kakanninku shi ya sa ya zaɓi zuriyarsu a bayansu, shi kansa kuma ya fisshe ku daga Masar da ikonsa mai girma.


“Ku kiyaye watan Abib don ku yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji Allahnku, gama a watan Abib ne Ubangiji Allahnku ya fito da ku daga Masar da dad dare.


Na aiki Musa da Haruna, na aukar wa Masar da annobai ta wurin abin da na yi a cikinta daga baya kuma na fisshe ku.


A shekara ta arbaminya da tamanin bayan fitowar mutanen Isra'ila daga ƙasar Masar, a shekara ta huɗu ta sarautar Sulemanu, Sarkin Isra'ila, a watan biyu, wato watan Zib, sai Sulemanu ya fara gina Haikalin Ubangiji.


Ubangiji kuwa ya fatattaki Habashawa a gaban Asa da Yahuza, Habashawa kuwa suka gudu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ