“Sai ku kiyaye idin abinci marar yisti har kwana bakwai a ƙayyadadden lokacinsa a watan Abib, gama a watan Abib kuka fito Masar. A lokacin za ku ci abinci marar yisti kamar yadda na umarce ku.
Wajibi ne ku yi idin abinci marar yisti, kamar yadda na umarce ku. Za ku ci abinci marar yisti kwana bakwai lokacin da aka ayyana a watan Abib, gama a wannan wata ne kuka fito daga Masar. Kada wani ya zo wurina hannu wofi.
A watan fari, wato watan Nisan, a shekara ta goma sha biyu ta sarautar sarki Ahasurus, sai suka yi ta jefa Fur, wato kuri'a, a gaban Haman kowace rana da kowane wata har kuri'a ta faɗo a kan watan goma sha biyu, wato watan Adar.
A faɗa wa dukan taron Isra'ilawa cewa, “A rana ta goma ga watan nan, kowane namiji ya ɗauki ɗan rago ko ɗan akuya daga cikin garke domin iyalinsa, dabba ɗaya domin kowane gida.
Musa ya ce wa jama'a, “Ku kiyaye wannan rana da kuka fito daga Masar, daga gidan bauta, gama da hannu mai ƙarfi Ubangiji ya fitar da ku daga wurin. Daɗai, ba za ku ci abinci mai yisti ba.