10 Kada ku bar kome ya kai gobe, abin da ya kai gobe kuwa, sai ku ƙone shi.
10 Kada ku bar kome yă kai gobe, abin da ya kai gobe kuwa, sai ku ƙone shi.
“Kada ku miƙa jinin hadayata tare da abinci mai yisti. Kada kuma ku ajiye kitsen abin da aka yanka a lokacin idina, ya kwana.
“Ba za ku miƙa jinin hadayata tare da abinci mai yisti ba, kada kuma a bar hadaya ta Idin Ƙetarewa ta kwana.
A ranar ce za a cinye, kada a bar kome ya kai gobe. Ni ne Ubangiji.
Amma idan naman keɓewar ko abincin ya ragu har safiya, sai ka ƙone abin da ya ragu, kada a ci, gama tsattsarka ne.
Musa ya ce musu, “Kada wani ya ci, ya bar saura har safiya.”
Kada su bar kome daga cikinsa ya kai gobe, kada kuwa a fasa ƙashinsa, sai su yi shi bisa ga dukan umarnin Idin Ƙetarewa.
A cinye ta a ranar da kuka miƙa ta ko kuwa kashegari. Abin da ya ragu har kwana na uku, sai a ƙone da wuta,