Sauran kwana biyu a yi Idin Ƙetarewa da idin abinci marar yisti, sai manyan firistoci da malaman Attaura suka nemi hanyar kama Yesu da makirci, su kashe shi,
Musa da Haruna suka aikata dukan waɗannan mu'ujizai a gaban Fir'auna. Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir'auna, bai kuwa saki Isra'ilawa daga ƙasarsa ba.
Sai suka kiyaye Idin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu ga watan farko da maraice a cikin jejin Sinai bisa ga dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa. Haka kuwa Isra'ilawa suka yi.
Wani annabi ya zo wurin Eli da saƙo daga wurin Ubangiji ya ce, “Sa'ad da kakanka Haruna da iyalinsa suke bauta wa Fir'auna a Masar, na bayyana kaina gare shi.
Yanzu fa, sai ka mayar wa mutumin da matarsa, gama shi annabi ne, zai yi maka addu'a, za ka kuwa rayu. In kuwa ba ka mayar da ita ba, ka sani hakika za ka mutu, kai, da dukan abin da yake naka.”