Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Fitowa 11:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Kowane ɗan farin da yake ƙasar Masar zai rasu, daga ɗan farin Fir'auna wanda zai hau gadon sarautarsa, har zuwa ɗan farin kuyanga wadda take niƙa, da dukan ɗan farin shanu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Kowane ɗan fari, namiji, a Masar zai mutu, daga kan ɗan fari na Fir’auna wanda zai ci gadon sarauta, har zuwa kan ɗan fari na baiwa, wadda take niƙa, da kuma dukan ’yan farin shanu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Fitowa 11:5
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya karkashe 'yan fari maza Na dukan iyalan da suke Masar.


Za a ga mata biyu suna niƙa, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya.


Shi ya karkashe 'ya'yan fari maza, na Masarawa, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.


A Masar ne ya karkashe 'ya'yan fari na mutane da na dabbobi.


Ya karkashe dukan 'ya'yan fari maza Na dukan iyalan Masarawa.


Gama sa'ad da Fir'auna ya taurare zuciyarsa, bai yarda ya sallame mu ba, Ubangiji kuwa ya kashe dukan 'ya'yan farin ƙasar Masar, na mutum da na dabba gaba ɗaya. Domin haka muke yin hadaya ga Ubangiji da 'ya'yan fari, maza, da suka fara buɗe mahaifa, amma mukan fanshi dukan 'ya'yan farinmu, maza.’


Da tsakar dare sai Ubangiji ya karkashe dukan 'ya'yan fari maza a ƙasar Masar, tun daga ɗan farin Fir'auna, wato magajinsa, har zuwa ɗan farin ɗan sarka da yake a kurkuku, har da dukan 'ya'yan fari maza na dabbobi.


A daren nan zan ratsa ƙasar Masar, in bugi kowane ɗan fari na ƙasar, na mutum da na dabba. Zan hukunta gumakan Masar duka, gama ni ne Ubangiji.


Na ce maka ka bar ɗana ya tafi domin ya bauta mini, amma in ka ƙi ka bar shi ya tafi, yanzu zan kashe ɗan fārinka.’ ”


Ta wurin bangaskiya ya ci Jibin Ƙetarewa, ya yayyafa jini, domin kada mai hallakar da 'ya'yan fari ya taɓa Isra'ilawa.


An tilasta wa samari su yi niƙa, Yara kuma suna tagataga da kayan itace.


Ki juya dutsen niƙa, ki niƙa gari! Ki kware lulluɓi! Ki tuɓe kyawawan tufafinki!


Filistiyawa fa suka kama shi, suka ƙwaƙule idanunsa, suka gangara da shi zuwa Gaza. Suka ɗaure shi da sarƙoƙin tagulla. Ya yi ta niƙa a kurkuku.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ