Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Fitowa 11:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Ubangiji kuwa ya sa jama'a su yi farin jini a idanun Masarawa. Musa kuwa ya zama babban mutum a ƙasar Masar a gaban fādawan Fir'auna da kuma gaban jama'ar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 (Ubangiji ya sa mutane suka sami tagomashi a idon Masarawa, Musa kuwa ya sami girma sosai a cikin ƙasar Masar a gaban fadawan Fir’auna da kuma a gaban jama’ar.)

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Fitowa 11:3
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji ya sa jama'a su yi farin jini a wurin Masarawa, saboda haka Masarawa suka ba su abin da suka roƙa. Ta haka suka washe Masarawa.


“Zan sa wannan jama'a su yi farin jini a idanun Masarawa, sa'ad da kuka fita kuma, ba za ku fita hannu wofi ba.


To, ga shi, zan sa su waɗanda suke daga jama'ar Shaiɗan, masu cewa su Yahudawa ne, alhali kuwa ba su ba ne, ƙarya suke yi, zan sa su, su zo, su kwanta a gabanka, su sani dai na ƙaunace ka.


'Ya'ya maza na waɗanda suka zalunce ki za su zo, Su rusuna, su nuna bangirma. Dukan waɗanda suka raina ki za su yi sujada a ƙafafunki. Za su ce da ke, ‘Birnin Ubangiji,’ ‘Sihiyona, Birni na Allah Mai Tsarki na Isra'ila.’


Ubangiji ya sa waɗanda suka kama su Su ji tausayinsu.


Amma Ubangiji yana tare da Yusufu, ya kuwa nuna masa madawwamiyar ƙauna, ya sa ya sami farin jini a wurin yarin kurkukun.


Sai aka karantar da Musa dukan ilimin Masarawa, shi kuwa mutum mai iko ne a cikin magana da ayyukansa.


Gama Mordekai ya zama babban mutum a gidan sarki, ya kuma yi suna a dukan larduna, gama ya yi ta ƙasaita gaba gaba.


Ban kuwa rabu da kai ba duk inda ka tafi, na kuma kawar da abokan gābanka duka. Zan sa ka shahara kamar shahararrun mutane na duniya.


Ubangiji ya aike shi ya aikata alamu da mu'ujizai a ƙasar Masar a gaban Fir'auna da dukan barorinsa, da dukan ƙasarsa.


Zan kuwa maishe ka al'umma mai girma, zan sa maka albarka, in sa ka ka yi suna, domin ka zama sanadin albarka.


Isra'ilawa kuwa suka yi yadda Musa ya faɗa musu, suka roƙi Masarawa kayan adonsu na azurfa da na zinariya, da kuma tufafi.


Tun daga lokacin nan, ba a taɓa yin wani annabi a Isra'ila kamar Musa ba, wanda Ubangiji ya san shi fuska da fuska.


A ranan nan Ubangiji ya ɗaukaka Joshuwa a idon dukan Isra'ilawa, har suka ga kwarjininsa dukan kwanakin ransa kamar yadda suka ga na Musa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ