“Zan mayar muku da abin da kuka yi hasararsa A shekarun da fara ta cinye amfaninku, Wato ɗango da fara mai gaigayewa, da mai cinyewa, Su ne babbar rundunata wadda na aiko muku.
Saboda haka Musa da Haruna suka tafi gaban Fir'auna suka ce masa, “Ga abin da Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya ce, ‘Har yaushe za ka ƙi yarda ka ba da kanka a gare ni? Saki jama'ata don su tafi su yi mini sujada.
za ta rufe fuskar ƙasar, har da ba za a iya ganin ƙasa ba. Za ta cinye sauran abin da ya kuɓuta daga ɓarnar ƙanƙara, za su cinye dukan itatuwan da suke girma a ƙasar.
Bayan wannan Musa da Haruna suka tafi gaban Fir'auna, suka ce, “Ga abin da Ubangjiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘Bar jama'ata su tafi domin su yi mini idi cikin jeji.’ ”