Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Sa'ad da ka koma Masar, sai ka kula, ka aikata a gaban Fir'auna dukan mu'ujizan da na sa cikin ikonka. Amma zan taurara zuciyarsa, don kada ya bar jama'a su fita.
Zan taurare zuciyar Fir'auna, zai kuwa bi ku, ni Ubangiji zan nuna ɗaukakata a bisa Fir'auna da dukan rundunansa. Masarawa kuwa za su sani ni ne Ubangiji.” Haka kuwa Isra'ilawa suka yi.
Sauran 'yan adam waɗanda bala'in nan bai kashe ba kuwa, ba su tuba sun rabu da abubuwan da suka yi da hannunsu ba, ba su kuma daina yin sujada ga aljannu, da gumakan zinariya, da na azurfa, da na tagulla, da na dutse, da na itace ba, waɗanda ba su iya gani, ko ji, ko tafiya,
Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Je ka wurin Fir'auna, gama na riga na taurare zuciyarsa da ta fādawansa domin in aikata waɗannan mu'ujizai nawa a tsakiyarsu,
Musa da Haruna suka aikata dukan waɗannan mu'ujizai a gaban Fir'auna. Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir'auna, bai kuwa saki Isra'ilawa daga ƙasarsa ba.