Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Fitowa 10:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Fir'auna ya aika da gaggawa a kira Musa da Haruna. Ya ce musu, “Na yi wa Ubangiji Allahnku zunubi, na kuma yi muku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Fir’auna ya kira Musa da Haruna da gaggawa ya ce, “Na yi wa Ubangiji Allahnku zunubi, na kuma yi muku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Fitowa 10:16
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Fir'auna ya aika, aka kirawo Musa da Haruna, ya ce musu, “Lalle a wannan karo na yi laifi, Ubangiji shi ne da gaskiya. Ni da jama'ata muke da kuskure.


ya ce, “Na yi zunubi da na ba da marar laifi a kashe shi.” Suka ce, “Ina ruwanmu? Kai ka jiyo!”


Ba za ka taɓa cin nasara a zamanka ba muddin kana ɓoye laifofinka. Ka hurta zunubanka ka tuba, sa'an nan Allah zai yi maka jinƙai.


Gama na sani, ranka ya daɗe, na yi laifi, shi ya sa na zama na farko daga gidan Yusufu yau da na fito domin in taryi ubangijina sarki.”


Sa'an nan Saul ya ce, “Na yi laifi, ka komo, ɗana Dawuda, ba zan yi maka kome ba, gama raina ya zama da daraja a gare ka kyau. Na yi aikin wauta, na yi laifi da yawa.”


Sai Saul ya ce, “Na yi zunubi, amma duk da haka ka darajanta ni a gaban shugabannin mutanena, da gaban Isra'ilawa, ka zo, mu tafi tare domin in yi wa Ubangiji Allah sujada.”


Sa'an nan Saul ya ce wa Sama'ila, “Na yi zunubi, na yi rashin biyayya ga umarnin Ubangiji da kuma koyarwarsa. Na ji tsoron mutanena, na kuwa biye wa abin da suke so.


Sai Bal'amu ya ce wa mala'ikan Ubangiji, “Na yi zunubi, gama ban sa ka tsaya a hanya don ka tarye ni ba. Yanzu fa, idan ka ga mugun abu ne, to, sai in koma.”


Jama'a kuwa suka zo wurin Musa, suka ce, “Mun yi zunubi gama mun yi wa Ubangiji gunaguni, mun kuma yi maka. Ka roƙi Ubangiji ya kawar mana da macizan.” Musa kuwa ya yi roƙo domin jama'ar.


Sai Fir'auna ya kirawo Musa da Haruna, ya ce su roƙi Ubangiji ya kawar masa da kwaɗin, shi da mutanensa, sa'an nan zai saki jama'ar, su tafi su miƙa wa Ubangiji hadaya.


Sa'an nan Fir'auna ya kirawo Musa da Haruna, ya ce, “Tafi, ku yi wa Allahnku hadaya a ƙasan nan.”


Bayan da Dawuda ya ƙidaya mutane, sai lamirinsa ya kā da shi, ya ce wa Ubangiji, “Na yi laifi ƙwarai a kan abin da na yi. Ina roƙonka, ya Ubangiji, ka gafarta mini, gama na yi wauta.”


Da Dawuda ya ga mala'ika wanda yake hallakar da mutanen, sai ya ce wa Ubangiji, “Na yi laifi, na aikata mugunta, amma me waɗannan tumaki suka yi? Ina roƙonka, ka hukunta ni da gidan ubana.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ