8 A wannan lokaci kuwa aka yi wani sabon sarki a Masar wanda bai san Yusufu ba.
8 Sai wani sabon sarki wanda bai san Yusuf ba, ya hau sarautar Masar.
har aka yi wani sarki a Masar, wanda bai san ko wane ne Yusufu ba.
Akwai wani matalauci, mai hikima, a garin, sai ya ceci garin ta wurin hikimarsa. Duk da haka ba wanda ya tuna da wannan matalauci.
Wannan sarki kuwa ya cuci kabilarmu, yana gwada wa kakanninmu tasku, yana sawa a yar da jariransu, don kada su rayu.
Masarawa suka wulakanta mu, suka tsananta mana, suka bautar da mu.
Ya sa Masarawa suka ƙi jinin jama'arsa, Suka yi wa bayinsa munafunci.
Ubangiji kuwa ya ce, “Na ga wahalar jama'ata waɗanda suke a Masar, na kuma ji kukansu da suke yi a kan shugabanninsu. Na san wahalarsu,
Yanzu fa, ga shi, kukan jama'ar Isra'ila ya zo gare ni. Na kuma ga wahalar da Masarawa suke ba su.
Tafi, ka tattara dattawan Isra'ila, ka faɗa musu, ‘Ubangiji Allah na kakanninku ya bayyana gare ni, wato na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, ya ce, sosai ya ziyarce ku, ya kuma ga abin da ake yi muku a Masar.
Dukan tsarar Joshuwa sun rasu, waɗanda suke tasowa kuwa suka manta da Ubangiji da abubuwan da ya yi wa Isra'ila.