5 Zuriyar Yakubu duka mutum saba'in ne, Yusufu kuwa, an riga an kai shi Masar.
5 Zuriyar Yaƙub duka sun kai mutum saba’in. Yusuf ya riga ya kasance a Masar.
Kakanninku saba'in ne suka gangara zuwa Masar, amma yanzu Ubangiji Allahnku ya riɓaɓɓanya ku, kuka yi yawa kamar taurarin sama.”
Yana kuma da 'ya'ya maza saba'in, gama yana da mata da yawa.
Allah kuwa ya yi wa ungozoman nan alheri. Mutanen suka riɓanya, suka ƙasaita ƙwarai.
Sai Yusufu ya aika wa ubansa Yakubu yă zo, da kuma dukan 'yan'uwansa, mutum saba'in da biyar.
da Dan, da Naftali, da Gad, da Ashiru.
Haka fa Yusufu ya zauna a Masar, shi da iyalin gidan mahaifinsa. Yusufu kuwa ya yi shekara ɗari da goma a duniya.