Idan za ka kasa kunne ga duk abin da na umarce ka, ka bi tafarkuna, ka aikata abin da yake daidai a gare ni, ka kiyaye dokokina da umarnaina kamar yadda bawana Dawuda ya yi, zan kasance tare da kai, zan sa gidanka ya kahu kamar yadda na sa gidan Dawuda ya kahu, zan ba ka Isra'ila.
Zan zaɓar wa kaina amintaccen firist wanda zai aikata abin da nake so ya yi, zan kuwa ba shi zuriya da ko yaushe za su yi aiki a gaban zaɓaɓɓen sarkina.
Ina roƙonka ka gafarta mini laifina. Ubangiji zai sa ka zama sarki, kai da zuriyarka, kana yin yaƙi na Ubangiji. Ba kuwa za ka aikata wani mugun abu ba a dukan kwanakinka.