15 Sarkin Masar ya ce wa ungozomar Ibraniyawa, Shifra da Fu'a,
15 Sai Sarkin Masar ya gaya wa ungozomomin matan Ibraniyawa, wato, su Shofra da Fuwa ya ce,
Suka baƙanta musu rai da aiki mai tsanani na kwaɓa, da yin tubali, da kowane irin aiki a saura. A cikin ayyukansu duka suka tsananta musu.
“Sa'ad da kuke yi wa matan Ibraniyawa hidimarku ta ungozomai, in kuka gan su durƙushe, in jariri ne suka haifa, sai ku yi masa sanadin mutuwa, in kuma jaririya ce, ku bar ta da rai.”
Sai Yunusa ya ce, “Ni Ba'ibrane ne, ina bin Ubangiji Allah na Sama, wanda ya yi teku da ƙasa.”
Gama ta riga ta kai su bisa rufin ɗaki, ta rufe su da ƙasheshen rama waɗanda ta shimfiɗa a bisa rufin.