Sai na ce masa, “Ya shugaba, ai, ka sani.” Sai ya ce mini, “Su ne waɗanda suka fito daga matsananciyar wahala, sun wanke rigunansu, suka mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan.
sai mu matsa kusa, da zuciya ɗaya, da cikakkiyar bangaskiya tabbatacciya, da zukatunmu tsarkakakku daga mugun lamiri, jikinmu kuma wankakke da tsattsarkan ruwa.
Sa'ad da suke shiga cikin alfarwa ta sujada ko sa'ad da suke kusatar bagade don su miƙa hadaya ta ƙonawa da wuta ga Ubangiji, sai su yi wanka don kada a kashe su.
Sa'an nan Ubangiji ya ba Musa ka'idodin nan. Sai Haruna ya sa zilaika ta lilin tsattsarka, ya ɗaura mukuru na lilin, ya yi ɗamara da abin ɗamara na lilin, ya naɗa rawani na lilin, waɗannan su ne tsattsarkar sutura. Zai yi wanka da ruwa, sa'an nan ya sa su.