5 Musa ya faɗa wa taron jama'ar cewa “Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta a yi.”
5 Sai Musa ya ce wa jama’ar, “Ga abin da Ubangiji ya umarta a yi.”
Musa kuwa ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi. Jama'ar kuwa suka tattaru a ƙofar alfarwa ta sujada.
Sai Musa ya fito da Haruna da 'ya'yansa maza, ya yi musu wanka.