34 Abin da aka yi a wannan rana haka Ubangiji ya umarta a yi domin kafararku.
34 Abin da aka yi a yau umarni ne daga Ubangiji don yin kafara saboda ku.
Ba zai miƙa hadaya kowace rana kumar waɗancan manyan firistocin ba, wato, da farko saboda zunubansa, sa'an nan kuma saboda na jama'a. Wannan ya yi ta ne sau ɗaya tak, lokacin da ya miƙa kansa hadaya.
wanda kuwa ya zama firist, ba bisa ga wata ka'ida ta al'adar 'yan adam ba, sai dai ta wurin ikon rai marar gushewa.
Ba za ku fita daga cikin alfarwa ta sujada ba har kwana bakwai, wato, sai kwanakin keɓewarku sun cika, gama keɓewarku za ta ɗauki kwana bakwai.
A ƙofar alfarwa ta sujada za ku zauna dare da rana har kwana bakwai, kuna kiyaye umarnin Ubangiji don kada ku mutu, gama haka Ubangiji ya umarta.”