Dukan taron Yahuza, da firistoci, da Lawiyawa, da dukan taron jama'a da suka zo daga Isra'ila, da baƙi waɗanda suka zo daga ƙasar Isra'ila, da baƙin da suka zauna a Yahuza, suka yi murna.
Sarki Sulemanu da dukan taron mutanen Isra'ila waɗanda suka hallara a gaban akwatin suka yi ta miƙa hadayun tumaki da bijimai masu yawan gaske, har ba su ƙidayuwa.
Sulemanu kuwa ya tattara dattawan Isra'ila, da shugabannin kabilai, da shugabannin gidajen kakannin jama'ar Isra'ila, a Urushalima, domin a yi bikin fito da akwatin alkawari na Ubangiji da yake a alfarwa a birnin Dawuda, wato Sihiyona.
Haka fa, Dawuda ya tattara dukan Isra'ilawa wuri ɗaya, daga Shihor ta Masar, har zuwa mashigin Hamat domin a kawo akwatin alkawari na Allah daga Kiriyat-yeyarim.
“Ka ɗauki sandanka, kai da Haruna, ɗan'uwanka, ku tara jama'a, ku yi magana da dutsen a gabansu ya ba da ruwan da yake cikinsa. Za ka sa ruwa ya ɓuɓɓugo musu daga dutsen. Ta haka za ka ba taron jama'a da garkunansu ruwan sha.”