Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 8:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Musa kuwa ya yanka shi, ya ɗibi jinin, ya sa a leɓatun kunnen dama na Haruna, da bisa babban yatsansa na hannun dama, da babban yatsa na ƙafar dama.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Musa kuwa ya yanka ɗan ragon ya ɗibi jinin ya sa leɓatun kunnen dama na Haruna, ya kuma sa a babbar yatsarsa ta hannun dama da kuma a babbar yatsar ƙafarsa ta dama.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 8:23
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'an nan ka yanka ragon, ka ɗibi jininsa ka shafa bisa leɓatun kunnen Haruna na dama, da bisa leɓatun kunnuwan 'ya'yansa maza na dama, da a kan manyan yatsotsin hannuwansu na dama, da kuma a kan manyan yatsotsin ƙafafunsu na dama. Sauran jinin kuwa, sai ka yayyafa shi a kewaye a kan bagaden.


Sauran man da ya ragu a tafin hannunsa, sai ya shafa shi a leɓatun kunnen dama na wanda za a tsarkake, da bisa babban yatsan hannunsa na dama, da na ƙafar dama. Wato, za a shafa man a inda aka shafa jinin hadaya don laifin.


Firist zai ɗibi jinin hadaya don laifi ya shafa a leɓatun kunnen dama, da bisa babban yatsan hannun dama, da na ƙafar dama na wanda za a tsarkake ɗin.


Ko da za a tsiyaye jinina a kan hadaya da hidima na bangaskiyarku, sai in yi farin ciki, in kuma taya ku farin ciki, ku duka.


Don kuwa ina ɗoki, ina kuma sa zuciya, ko kaɗan ba zan kunyata ba, sai dai zan yi ƙarfin hali matuƙa a yanzu kamar koyaushe, a girmama Almasihu a jikina, ko ta wurin rayuwata, ko ta wurin mutuwata.


Sayenku aka yi da tamani. To, sai ku ɗaukaka Allah da jikinku.


Gama Allah ne ya sa kuka zama na Almasihu Yesu, Allah ne kuma ya sa Almasihu ya zama hikima a gare mu. Ta wurin Almasihu ne kuma muka sami adalci, da tsarkakewa da fansa.


zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Koranti, wato, su waɗanda aka keɓe a cikin Almasihu Yesu, tsarkaka kirayayyu, tare da dukan waɗanda a ko'ina suke addu'a, da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangijinsu da namu duka.


Don haka ina roƙonku 'yan'uwa, saboda yawan jinƙai na Allah, ku miƙa jikinku hadaya rayayyiya, tsattsarka, abar karɓa ga Allah. Domin wannan ita ce ibadarku ta ainihi.


Mai da magana nake yi irin ta yau da kullum, saboda rarraunar ɗabi'arku. Wato, kamar yadda dā can kuka miƙa gaɓoɓinku ga bautar rashin tsarki, da mugun aiki a kan mugun aiki, haka kuma a yanzu sai ku miƙa gaɓoɓinku ga bautar aikin adalci, domin aikata tsarkakan ayyuka.


Kada kuma ku miƙa gaɓoɓinku su zama kayan aikin mugunta, don yin zunubi. Amma ku miƙa kanku ga Allah, kamar waɗanda aka raya bayan mutuwa, kuna miƙa gaɓoɓinku ga Allah kayan aikin adalci.


Ya kuma shafa man da ya ragu cikin hannunsa a leɓatun kunnen dama na wanda za a tsarkake, da a babban yatsan hannun damansa, da kuma a babban yatsan ƙafar damansa, a inda aka shafa jinin hadaya don laifin.


Ko da yake shi Ɗa ne, ya koyi biyayya ta wurin wuyar da ya sha,


Saboda haka, ya dace da Allah, shi da dukkan abubuwa suka kasance dominsa, ta gare shi ne kuma dukkan abubuwa suka samu, yă kammala shugaban cetonsu ta wurin shan wuya, a wajen kawo 'ya'ya masu yawa ga samun ɗaukaka.


Ka ɗiba daga cikin jinin da yake bisa bagaden, da man keɓewa, ka yayyafa wa Haruna da tufafinsa, da bisa 'ya'yansa maza, da tufafinsu don a tsarkake Haruna, da 'ya'yansa maza, da tufafinsu.


Waɗannan su ne ka'idodin hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta gari, da hadaya don zunubi, da hadaya don laifi, da hadaya don keɓewa, da hadaya ta salama.


Sa'an nan ya yanka ɗan ragon don laifi, ya ɗibi jinin hadaya don laifin, ya shafa a leɓatun kunnen dama na mutumin da za a tsarkake, da a babban yatsan hannunsa na dama, da ƙafarsa ta dama.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ