“Abin da za ka yi wa Haruna da 'ya'yansa ke nan don ka keɓe su su zama firistoci masu yi mini aiki. Za ka ɗauki ɗan bijimi da raguna biyu marasa lahani,
“Daga cikin 'ya'ya maza na Isra'ila sai ka kirawo ɗan'uwanka Haruna tare da 'ya'yansa, Nadab, da Abihu, da Ele'azara, da Itamar, su zama firistoci masu yi mini aiki.
Amma Haruna da 'ya'yansa maza suka miƙa hadayu a kan bagaden hadaya ta ƙonawa, da kan bagaden ƙona turare, domin dukan aikin Wuri Mafi Tsarki, da kuma yin kafara domin Isra'ila bisa ga dukan abin da Musa, bawan Allah, ya umarta.