Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 7:37 - Littafi Mai Tsarki

37 Waɗannan su ne ka'idodin hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta gari, da hadaya don zunubi, da hadaya don laifi, da hadaya don keɓewa, da hadaya ta salama.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

37 Waɗannan su ne ƙa’idodi don hadaya ta ƙonawa, hadaya ta gari, hadaya don zunubi, hadaya don laifi, hadaya ta naɗi da kuma hadaya ta salama,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 7:37
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Abin da za ka yi wa Haruna da 'ya'yansa ke nan don ka keɓe su su zama firistoci masu yi mini aiki. Za ka ɗauki ɗan bijimi da raguna biyu marasa lahani,


domin keɓe firist, wato, zuriyar Haruna. A ranar da za a keɓe shi zai kawo humushin garwar gari mai laushi (kamar yadda akan kawo na hadaya ta gari), za a miƙa rabinsa da safe, rabin kuma da maraice.


Ubangiji ya kirawo Musa, ya yi masa magana daga cikin alfarwa ta sujada, ya ce


“Sai ka ɗebe kitsen ragon, ka yanke wutsiyarsa mai kitse, ka kuma ɗebe kitsen da yake rufe da kayan ciki, da dunƙulen kitsen da yake a bisa hanta, da ƙoda biyu ɗin da kitsensu, da cinyar dama, gama ragon na keɓewa ne.


Amma idan 'yar tunkiyar ta fi ƙarfinsa, sai ya kawo kurciyoyi biyu ko 'yan tattabarai biyu don yin hadaya ga Ubangiji saboda laifin da ya yi. Ɗaya za ta zama ta yin hadaya don laifi, ɗayan kuwa don yin hadaya ta ƙonawa.


Musa ya kawo ɗayan ragon keɓewa, sai Haruna da 'ya'yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan kan ragon.


Musa kuwa ya yanka shi, ya ɗibi jinin, ya sa a leɓatun kunnen dama na Haruna, da bisa babban yatsansa na hannun dama, da babban yatsa na ƙafar dama.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ