Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 7:34 - Littafi Mai Tsarki

34 Gama Ubangiji ya ba Haruna da 'ya'yansa maza, ƙirjin da aka kaɗa da cinyar da aka ɗaga, su zama rabonsu daga cikin hadayu na salama na Isra'ilawa. Ya ba Haruna, firist, da 'ya'yansa maza, su zama rabonsu har abada daga cikin hadayu na Isra'ilawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

34 Daga hadaya ta salama ta Isra’ilawa, na ɗauki ƙirjin da aka kaɗa da kuma cinyar da aka miƙa, na ba da su ga Haruna firist da kuma ’ya’yansa maza a matsayin rabonsu na kullum daga Isra’ilawa.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 7:34
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“To, ga rabon da jama'a za su ba firistoci daga hadayun da suka miƙa, ko sā ne ko tunkiya ce, sai su ba firistoci kafaɗar, da kumatun, da tumbin.


Ba za a ci kitse ko jinin ba a wuraren zamanku. Wannan doka madawwamiya ce.


Ka kuma ɗaura musu ɗamara, ka sa musu hulunan. Aikin firist kuwa zai zama nasu har abada bisa ga dokar. Haka za ka keɓe Haruna da 'ya'yansa maza.


“Za ka ɗauki ƙirjin ragon da aka yanka don keɓewar Haruna, ka kaɗa shi don hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji. Wannan ƙirji zai zama rabonka.


Cinyar ƙafar dama za ta zama rabon ɗan Haruna wanda ya miƙa jinin da kitsen hadaya ta salama.


Dukan sadakoki na tsarkakakkun abubuwa na Isra'ilawa waɗanda sukan kawo wa firist, za su zama nasa.


Haruna kuma zai gabatar da Lawiyawan a gaban Ubangiji kamar hadaya ta kaɗawa daga Isra'ilawa domin su zama masu yi wa Ubangiji aiki.


Firist ɗin zai haɗa su don yin hadayar kaɗawa a gaban Ubangiji. Za su zama rabo mai tsarki na firist tare da ƙirjin da aka kaɗa da cinyar da aka yi hadayar ɗagawa da ita. Bayan haka keɓaɓɓen ya iya shan ruwan inabi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ