'Ya'yan Haruna, maza kuwa, za su ƙone su tare da hadayar ƙonawa da take bisa itacen da yake cikin wutar bagade, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
Firist ɗin zai ɗauki dafaffiyar kafaɗar ragon, da malmala guda marar yisti daga cikin kwando, da ƙosai guda, ya sa su a tafin hannun keɓaɓɓen bayan da keɓaɓɓen ya riga ya aske sumarsa.
Ubangiji ya kuma ce wa Haruna, “Na ba ka aikin lura da hadayuna na ɗagawa, wato sadakokin Isra'ilawa, na ba ka su su zama rabonka da na 'ya'yanka har abada.