Firistoci 7:18 - Littafi Mai Tsarki18 Idan aka ci naman hadayarsa ta salama a rana ta uku, ba za a karɓi wanda ya ba da hadayar har ya sami fa'idar hadayar ba, naman zai zama abin ƙyama, duk wanda ya ci ya yi laifi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202018 Idan aka ci naman hadayarsa ta salama a rana ta uku, ba za a karɓi wanda ya ba da hadayar har ya sami albarkar hadayar ba, naman zai zama abin ƙyama, duk wanda ya ci kuwa ya yi laifi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Mutane suna yin abin da suka ga dama. Suna kashe bijimi domin hadaya, ko su yi hadaya da mutum. Sukan yi hadaya da ɗan rago, ko kuwa su karye wuyan kare. Sukan miƙa hadaya ta hatsi, ko kuwa su miƙa jinin alade. Suna miƙa turare, ko kuwa su yi addu'a ga gumaka. Suna jin daɗin al'amuran banƙyama a lokacin yin sujada.