ya ba Haruna da 'ya'yansa maza waɗannan ka'idodi domin hadaya don zunubi. A inda ake yanka hadaya ta ƙonawa, a nan ne za a yanka hadaya don zunubi a gaban Ubangiji, hadaya ce mai tsarki.
Ba za a sa masa yisti a toya shi ba. Wannan Ubangiji ne ya ba su ya zama rabonsu daga cikin hadayun da ake ƙonawa da wuta, abu ne mafi tsarki, kamar hadaya don zunubi da laifi.
Sai ya ce mini, “Wannan shi ne wurin da firistoci za su dafa hadaya domin laifi, da hadaya domin zunubi, a nan ne kuma za su toya hadaya ta gāri, domin kada su kai su a filin waje, su sa wa mutane tsarki.”
Sai ya sāke keɓe kansa ga Ubangiji daidai da kwanakin da ya ɗauka a dā. Zai kawo ɗan rago bana ɗaya na yin hadaya don laifi. Kwanakin da ya yi a dā ba su cikin lissafi domin keɓewarsa ta dā ta ƙazantu.
Amma idan har kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu sun fi ƙarfinsa don yin hadaya saboda laifinsa, sai ya kawo humushin garwar gari mai laushi don yin hadaya saboda laifinsa. Ba zai zuba mai ko lubban a garin ba, gama hadaya ce don laifi.
Amma idan 'yar tunkiyar ta fi ƙarfinsa, sai ya kawo kurciyoyi biyu ko 'yan tattabarai biyu don yin hadaya ga Ubangiji saboda laifin da ya yi. Ɗaya za ta zama ta yin hadaya don laifi, ɗayan kuwa don yin hadaya ta ƙonawa.
Idan mutum ya ci amana, ya kuwa yi laifi ba da gangan ba, a kan tsarkakakkun abubuwa na Ubangiji, sai ya kawo rago marar lahani daga garken tumaki ga Ubangiji saboda yin hadaya don laifinsa. Za a kimanta ragon da tamanin kuɗi bisa ga ma'aunin azurfar da ake aiki da shi.
Kore kuwa ɗan Imna Balawe, mai tsaron ƙofar gabas, yake lura da hadayu na yardar rai ga Allah, don ya karkasa bayarwar da aka keɓe domin Ubangiji da hadayu mafi tsarki.