Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 6:4 - Littafi Mai Tsarki

4 sa'ad da mutum ya yi laifi, ya kuwa tabbata mai laifi ne, sai ya mayar da abin da ya ƙwace, ko abin da ya samu ta hanyar zalunci, ko abin da aka ba shi ajiya, ko abin da ya tsinta,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 sa’ad da mutum ya yi irin laifin nan, ya kuwa tabbata mai laifi ne, to, sai yă komar da abin da ya ƙwace, ko abin da ya samu ta hanyar zalunci, ko abin da aka ba shi ajiya, ko abin da ya tsinta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 6:4
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A wannan rana zan hukunta duk wanda yake tsalle a bakin ƙofa, Da waɗanda suke cika gidan maigidansu da zalunci da ha'inci.


Sukan yi ƙyashin gonaki da gidaje, sai su ƙwace. Sukan zalunci mutum, su ƙwace gidansa da gādonsa.


Ubangiji ya ce, “Waɗannan mutane suka cika gidajensu masu daraja da abubuwan da suka samo ta hanyar zamba, da ta kama-karya. Ta yadda za su yi su yi aminci ma, ba su sani ba.


Amma mahaifinsa, da yake ya yi zalunci, ya yi wa ɗan'uwansa ƙwace ya aikata mugun abu a cikin mutanensa, zai mutu saboda muguntarsa.


yana kuma cin zalin matalauta masu fatara, yana yin ƙwace, ba ya mayar da abin da aka jinginar masa, yana bauta wa gumaka, yana kuma aikata abubuwa masu banƙyama,


wanda ba ya cin zalin kowa, wanda yakan mayar wa wanda ya ba shi jingina abin da ya jinginar masa, wanda ba ya ƙwace, amma yakan ba mayunwanci abinci, wanda yakan ba huntu tufa,


Saƙarku ba za ta yi amfani kamar tufa ba, ba za ku yi sutura da abin da kuka yi ba. Ayyukanku ayyukan mugunta ne, kuna aikata ayyukan kama-karya.


“Mugaye sukan ci iyaka, Don su ƙara yawan gonarsu. Sukan saci tumaki su zuba cikin garkunansu.


Saboda zalunci da rashin kula da matalauta, Da ƙwace gidajen da waɗansu suka gina.


Sa'ad da Ibrahim ya kawo kuka ga Abimelek a kan rijiyar ruwa wadda barorin Abimelek suka ƙwace,


Wanda ya kashe dabba kuma ya yi ramuwa, rai maimakon rai.


Wanda ya kashe dabba ya yi ramuwa, wanda kuwa ya kashe mutum sai a kashe shi.


sai ya hurta zunubinsa, sa'an nan ya biya cikakkiyar diyyar abin da ƙarin humushin abin, ya ba mutumin da ya yi wa laifin.


idan kuma ya mayar da jingina, ya mayar da abin da ya ƙwace, sa'an nan ya kiyaye dokokin rai, ya daina yin laifi, hakika, zai rayu, ba zai mutu ba.


Kuka kuma ce, ‘Mun gaji da wannan irin abu fa!’ Kuna hura mini hanci. Kukan kawo satacciyar dabba, ko gurguwa ko marar lafiya, ku yi mini hadaya da ita! Kuna tsammani zan karɓi wannan daga gare ku?


da sauran bijimin duka zai kai su waje bayan zango a wuri mai tsabta inda ake zubar da toka, nan zai ƙone su da wuta a inda ake zubar da tokar.


Yau sai ku mayar musu da gonakinsu, da gonakin inabinsu, da na zaitunsu, da gidajensu, da kashi ɗaya bisa ɗari na kuɗi, da na hatsi, da na ruwan inabi, da na mai, waɗanda kuka karɓa a wurinsu.”


Sa'ad da suka fita zuwa filin da yake waje, wurin mutane, sai su tuɓe tufafin da suka yi hidima da su, su ajiye su a tsarkakakkun ɗakuna, sa'an nan su sa waɗansu tufafi domin kada su tsarkake mutane da tsarkakakkun tufafinsu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ