Firistoci 6:25 - Littafi Mai Tsarki25 ya ba Haruna da 'ya'yansa maza waɗannan ka'idodi domin hadaya don zunubi. A inda ake yanka hadaya ta ƙonawa, a nan ne za a yanka hadaya don zunubi a gaban Ubangiji, hadaya ce mai tsarki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202025 “Faɗa wa Haruna da ’ya’yansa maza, ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi domin hadaya don zunubi. Za a yanka hadaya don zunubi a gaban Ubangiji a inda ake yankan hadaya ta ƙonawa; dole tă kasance mai tsarki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan ya ce mini, “Ɗakunan da suke wajen kudu da na wajen arewa gaban farfajiya, su ne tsarkakan ɗakuna inda firistoci waɗanda suke kusatar Ubangiji za su ci hadayu mafi tsarki. A nan kuma za su ajiye hadayu mafi tsarki, wato hadaya ta gari, da hadaya domin zunubi, da hadaya domin laifi, gama wurin tsattsarka ne.