Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 6:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Kowane ɗa namiji cikin 'ya'yan Haruna zai iya ci daga cikin hadayun Ubangiji waɗanda akan yi da wuta. Wannan madawwamiyar doka ce cikin zamananku duka. Duk wanda ya taɓa hadayu zai tsarkaka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 Kowane ɗa namiji cikin zuriyar Haruna zai iya cinsa. Wannan rabonsa ne na kullum na hadayar da aka yi ga Ubangiji da wuta. Wannan madawwamiyar doka ce cikin zamananku duka. Duk abin da ya taɓa hadayun zai tsarkaka.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 6:18
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A wuri mai tsarki za ku ci shi, kowane namiji ya iya ci. Abu mai tsarki ne a gare ka.


Kowane namiji a cikin firistoci zai iya cin naman, gama abu ne mafi tsarki.


Amma ku kabila ce zaɓaɓɓiya, ƙungiyar firistocin babban Sarki, tsattsarkar al'umma, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wannan da ya kirawo ku daga cikin duhu, kuka shiga maɗaukakin haskensa.


Domin a rubuce yake cewa, “Sai ku zama tsarkaka domin ni mai tsarki ne.”


Duk wanda ya taɓa naman zai tsarkaka, in kuma jinin ya ɗiga a riga, sai a wanke rigar a wuri mai tsarki.


Ba za a ci kitse ko jinin ba a wuraren zamanku. Wannan doka madawwamiya ce.


Kwana bakwai za ka ɗauka na yin kafara don bagaden, ka keɓe shi, haka kuwa bagaden zai zama mafi tsarki. Duk abin da ya taɓa bagaden zai tsarkaka.”


Ashe, ba ku sani ba, masu hidima a Haikali daga nan suke samun abincinsu? Masu hidimar bagadi kuma, a nan suke samun rabo daga hadayar da aka yanka?


Kowane namiji a cikin firistoci zai iya ci. Sai a wuri mai tsarki za a ci, gama tsattsarkan abu ne.


Ubangiji ya kuma ce wa Haruna, “Na ba ka aikin lura da hadayuna na ɗagawa, wato sadakokin Isra'ilawa, na ba ka su su zama rabonka da na 'ya'yanka har abada.


Idan keɓaɓɓen firist ne ya yi zunubi, ya jawo wa jama'a laifi, sai ya ba da ɗan bijimi marar lahani ga Ubangiji don yin hadaya saboda zunubin da ya aikata.


Zai ɗibiya hannunsa a kan kan bunsurun, ya yanka a wurin da ake yanka hadaya ta ƙonawa a gaban Ubangiji, gama hadaya ce don zunubi.


Zai ɗibiya hannunsa a kan kan abin yin hadaya don zunubin, sa'an nan ya yanka a wurin da akan yanka hadaya ta ƙonawa.


Firist zai sa rigarsa ta lilin, ya ɗaura mukurunsa na lilin, sa'an nan ya kwashe tokar hadaya ta ƙonawa daga bagaden, ya zuba a gefensa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ