Sai a bar wutar bagaden ta yi ta ci, kada a kashe ta. Firist ɗin ya yi ta iza wutar kowace safiya, ya shimfiɗa hadaya ta ƙonawa a jere a bisa wutar, ya kuma ƙone kitsen hadaya ta salama a bisanta.
Ɗakin da yake fuskantar arewa na firistoci ne waɗanda suke lura da bagade. Waɗannan su ne zuriyar Zadok waɗanda su kaɗai ne daga cikin Lawiyawa da suke da iznin kusatar Ubangiji don su yi masa hidima.”
“Abin da za ka yi wa Haruna da 'ya'yansa ke nan don ka keɓe su su zama firistoci masu yi mini aiki. Za ka ɗauki ɗan bijimi da raguna biyu marasa lahani,
Wuta kuma ta fito daga wurin Ubangiji, ta ƙone hadaya ta ƙonawa da kitsen a bisa bagaden. Da jama'a duka suka gani, suka yi ihu, suka fāɗi rubda ciki suka yi sujada.
Sarkinsu zai tsere saboda razana, shugabannin sojojinsu kuwa za su firgita, har su watsar da tutocinsu na yaƙi.” Ubangiji ne ya faɗa, Ubangiji da ake yi wa sujada a Urushalima, wanda kuma wutarsa tana ci a can domin hadayu.