Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 5:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Ko kuma idan ya taɓa kowace irin ƙazantar mutum wadda akan ƙazantu da ita, ba da saninsa ba, amma in daga baya ya sani, to, laifi ya kama shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Ko kuwa in ya taɓa rashin tsabta na mutane, wani abin da zai sa shi rashin tsabta; ko da yake bai sani ba, sa’ad da ya gane, zai zama mai laifi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 5:3
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ko kuma idan mutum ya taɓa kowane abin da yake haram ko mushen haramtacciyar dabba ta jeji ko ta gida, ko mushen haramtaccen abin da yake rarrafe, zai zama da laifi, ko da bai sani ba.


Ko kuma idan mutum ya yi rantsuwa da garaje da bakinsa, cewa, zai yi mugunta, ko nagarta, ko kowace irin rantsuwa ta garaje da mutane sukan yi, to, laifi ya kama shi bayan da ya gane da rantsuwarsa.


Idan wani mutum ya taɓa abu marar tsarki, ko mutum ne, ko dabba ce, ko wani abu na banƙyama, ya kuma ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji, za a raba wannan mutum da mutanensa.


Duk abin da mutumin da ba shi da tsarki ya taɓa zai ƙazantu, duk wanda kuma ya taɓa abin da marar tsarkin ya taɓa zai ƙazantu har maraice.”


A ranar da zai shiga Wuri Mai Tsarki, can fili na ciki, domin ya yi hidima a wurin, sai ya miƙa hadayarsa don zunubi, ni Ubangiji Allah na faɗa.


Firist ɗin zai dudduba cutar da take a fatar jikin mutumin. Idan gashin da yake wurin cutar ya rikiɗa ya zama fari, zurfin cutar kuma ya zarce fatar jikinsa, wannan cuta kuturta ce. Firist ɗin da ya dudduba shi zai hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ