Firistoci 5:15 - Littafi Mai Tsarki15 Idan mutum ya ci amana, ya kuwa yi laifi ba da gangan ba, a kan tsarkakakkun abubuwa na Ubangiji, sai ya kawo rago marar lahani daga garken tumaki ga Ubangiji saboda yin hadaya don laifinsa. Za a kimanta ragon da tamanin kuɗi bisa ga ma'aunin azurfar da ake aiki da shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202015 “Sa’ad da mutum ya ci amana, ya kuma yi zunubi ba da gangan ba dangane da wani cikin abubuwa masu tsarki na Ubangiji, zai kawo ga Ubangiji rago daga garke wanda ba shi da lahani saboda yin hadaya don laifinsa. Za a kimata kuɗinsa bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri. Hadaya ce ta laifi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Abin da aka ƙayyade za su biya bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi. Masu biya Abin da za su biya Maza masu shekara 20-60 Shekel hamsin Mata masu shekara 20-60 Shekel talatin Maza masu shekara 5-20 Shekel ashirin Mata masu shekara 5-20 Shekel goma sha biyar Maza masu wata guda zuwa shekara 5 Shekel biyar Mata masu wata guda zuwa shekara 5 Shekel uku Tsohon da ya fi shekara 60 Shekel goma sha biyar Tsohuwar da ta fi shekara 60 Shekel goma.