Ta haka firist zai yi kafara don laifin da mutumin ya aikata daga cikin abubuwan nan, za a kuwa gafarta masa. Sauran garin zai zama na firist kamar yadda yakan zama nasa a hadaya ta gari.
Idan mutum ya ci amana, ya kuwa yi laifi ba da gangan ba, a kan tsarkakakkun abubuwa na Ubangiji, sai ya kawo rago marar lahani daga garken tumaki ga Ubangiji saboda yin hadaya don laifinsa. Za a kimanta ragon da tamanin kuɗi bisa ga ma'aunin azurfar da ake aiki da shi.