Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 5:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Amma idan har kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu sun fi ƙarfinsa don yin hadaya saboda laifinsa, sai ya kawo humushin garwar gari mai laushi don yin hadaya saboda laifinsa. Ba zai zuba mai ko lubban a garin ba, gama hadaya ce don laifi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 “ ‘In ba zai iya kawo kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu ba, sai yă kawo humushin garwan gari mai laushi domin hadaya don zunubi. Ba lalle ba ne yă sa mai ko turare a kansa, saboda wannan hadaya ce ta zunubi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 5:11
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

duk da haka sai mutum ya kawo matarsa a gaban firist, ya kawo kuma hadayar da ake bukata, wato humushin garwar garin sha'ir, amma kada ya zuba mai ko kayan ƙanshi, gama hadaya ce domin kishi, domin a bayyana gaskiya a fili.


Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi zunubi saboda mu, domin mu mu sami adalcin Allah ta wurinsa.


Zai kai wa firist garin, firist zai ɗibi garin cike da tafin hannunsa, wannan shi ne kashi na tunawa. Zai ƙone shi bisa bagaden kamar hadaya na ƙonawa ga Ubangiji, gama hadaya ce don laifi.


Zai yayyafa jinin hadaya don laifi a gefen bagaden, sauran jinin kuwa zai tsiyaye a gindin bagade, gama hadaya ce don laifi.


Ya kuma kawo hadaya ga Ubangiji don laifin da ya yi. Sai ya kawo 'yar tunkiya ko akuya domin hadaya don zunubi. Firist zai yi kafara don laifin mutumin.


Amma da aka auna da mudu, ta waɗanda suka zarce ba ta yi saura ba, ta waɗanda ba su kai ba, ba ta gaza ba. Kowane mutum ya tattara daidai cinsa.


su kuma yi hadaya bisa ga abin da aka faɗa a Shari'ar Ubangiji cewa, “Kurciyoyi biyu, ko kuwa 'yan shila biyu.”


Hakika, bisa ga Shari'a, kusan kowane abu da jini ake tsarkake shi, in ba a game da zubar da jini ba kuwa, to, ba gafara.


Idan kuma hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji daga cikin tsuntsaye ne, sai ya kawo kurciyoyi, ko 'yan tattabarai.


domin keɓe firist, wato, zuriyar Haruna. A ranar da za a keɓe shi zai kawo humushin garwar gari mai laushi (kamar yadda akan kawo na hadaya ta gari), za a miƙa rabinsa da safe, rabin kuma da maraice.


Amma idan matalauci ne, har ba zai iya samun waɗannan abubuwa ba, sai ya kawo ɗan rago ɗaya domin hadaya don laifi, a yi hadaya ta kaɗawa, a yi kafara dominsa. Ya kuma kawo humushin garwa na gari mai laushi kwaɓaɓɓe da man zaitun don yin hadaya ta gari, da rabin moɗa na mai,


Idan mutumin ya cika talauci har ya kasa biyan tamanin da aka kimanta, sai ya kawo mutumin da aka yi wa'adi a kansa a gaban firist, firist ɗin zai kimanta tamaninsa daidai da ƙarfin wanda ya yi wa'adin.


Amma idan ɗan rago ya fi ƙarfinta, sai ta kawo kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu, ɗaya don hadaya ta ƙonawa, ɗayan kuwa don yin hadaya don zunubi. Firist kuwa zai yi kafara dominta, za ta kuwa tsarkaka.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ