Firistoci 4:3 - Littafi Mai Tsarki3 Idan keɓaɓɓen firist ne ya yi zunubi, ya jawo wa jama'a laifi, sai ya ba da ɗan bijimi marar lahani ga Ubangiji don yin hadaya saboda zunubin da ya aikata. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 “ ‘In shafaffen firist ya yi zunubi, ya jawo wa jama’a laifi, dole yă kawo wa Ubangiji ɗan bijimi marar lahani a matsayin hadaya don zunubi saboda zunubin da ya yi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Waɗanda fa suka komo daga zaman talala, suka miƙa wa Allah na Isra'ila hadaya ta ƙonawa, da bijimai goma sha biyu domin dukan Isra'ila, da raguna tasa'in da shida, da 'yan raguna saba'in da bakwai. Suka kuma miƙa hadaya don zunubi da bunsurai goma sha biyu. Dukan wannan ya zama hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.