Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 4:29 - Littafi Mai Tsarki

29 Zai ɗibiya hannunsa a kan kan hadaya don zunubi, ya yanka hadayar a wurin hadaya ta ƙonawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

29 Zai ɗibiya hannunsa a kan hadaya don zunubin yă kuma yanka ta a inda ake hadaya ta ƙonawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 4:29
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Zai ɗibiya hannunsa a kan kan bunsurun, ya yanka a wurin da ake yanka hadaya ta ƙonawa a gaban Ubangiji, gama hadaya ce don zunubi.


Zai kawo ɗan bijimin a ƙofar alfarwa ta sujada a gaban Ubangiji, ya ɗibiya hannunsa a kan kan bijimin, ya yanka shi a gaban Ubangiji.


Sai dattawan jama'a su ɗibiya hannunsu a kan kan bijimin a gaban Ubangiji, sa'an nan a yanka bijimin a gaban Ubangiji.


Sai ya ɗibiya hannunsa a kan kan hadaya ta ƙonawar, za a karɓa masa, a kuwa yi masa gafara.


Zai ɗibiya hannunsa a kan kan abin yin hadaya don zunubin, sa'an nan ya yanka a wurin da akan yanka hadaya ta ƙonawa.


Sa'an nan zai yanka ɗan bijimin a gaban Ubangiji. 'Ya'yan Haruna maza, firistoci, za su miƙa jinin a bagaden da yake a ƙofar alfarwa ta sujada za su kuma yayyafa jinin a kewaye da shi.


Zai yanka shi a arewacin bagaden a gaban Ubangiji. 'Ya'yan Haruna, firistoci, za su yayyafa jinin a kewaye da bagaden.


Ba a kawo kuɗi na hadaya don laifi da hadaya don zunubi a cikin Haikalin Ubangiji ba, ya zama na firistoci.


Sa'an nan suka kawo wa sarki da taron jama'a bunsuran yin hadaya domin zunubi, suka ɗora hannuwansu a kan bunsuran.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ